Cikin wannan Application, Audio ne na karatun littafin Hisnul Muslim wanda Sheik Aminu Ibrahim Daurawa Kano da kuma babban Malamin nan na Al-Qur'an Sheik Ahmad Sulaiman suka gabartar. Karatun ya qunshi sharhi da kuma karatun addu'o'i da suke cikin wannan littafi mai albarka da kuma yadda ake karantasu ba tare da kuskure ba,
Wannan Karatu zai taimakawa mai sauraro wajen fahimtar ma'anonin wadannan addu'o'i da kuma karantasu ta shiga ingantacciya tare da samun sauqi wajen haddace su.
Allah ya qara bamu ilimi mai amfani, ya kuma tabbatar damu akan tafarki madaidaici. Ameen.